Feb 08, 2019 19:14 UTC
  • An Gudanar Da Zaman Makoki Na Juyayin Shahadar Fatimah Zahra (s) A Gidan Jagora

An gudanar da zaman makoki na daren shahadar Fatimah Zahra (s) Diyar Manzon Allah (s) a Husainiyar Imam Khomanin(q) da ke gidan Jagoran juyin juya halin musulunci a daren yau Jumma'a.

Shafin yanar gizo na jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyed Aliyul Khamina'i ya bayyana cewa an gudanar da zaman makokin ne tare da halattar jagoran juyin juya halin musulunci da kuma wasu manya-manyan jami'an gwamnati da kuma mutane daga sassasa daban daban. 

A ranar 3 ga watan J-Thani shekara ta 11 ne Fatima Zahra (s) diyara Manzon Allah (s) ta yi shahada yan watanni bayan wafatin mahifinta manzon Allah (s). 

A na fara zaman makokin Fatimah (s) ne tun ranar 5a ga watan Febreru, sannan za'a kammala zaman makokin a gobe Asabar 9 ga watan Febreru wanda yayi dai-dai da 3 ga watan Jamada Thani na shekara ta 1440.H.K. 

Muna mika ta'aziyarmu ga masu sauraro ga wannan babban rashin. 

Tags

Ra'ayi