Feb 26, 2019 06:24 UTC
  • Taimakawa Siriya Yana A Matsayin Gwagwarmaya

Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran ya ce; taimakawa kasar Syria gwamnati da al’ummarta yana a matsayin gwagwarmaya ne wacce take abin alfahari.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kasar Syria Basshar Assad wanda ya kawo ziyarar aiki Iran  a jiya Litinin.

Jagoran juyin musuluncin na Iran ya kara da cewa; sirrin nasarar da gwamnati da kuma al’ummar Syria su ka samu akan Amurka da ‘yan korenta na wannan yankin shi ne tsayin da jajurcewa.

Har ila yau jagoran ya ja hankalin al’ummar Syria da su kasance cikin fadaka dangane da wani makircin da makiya za su iya sake kitsa musu.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma ce; Iran za ta ci gaba da kasancewa a tare da Syria saboda kasa ce wacce ta yi tsayin daka akan tafarkin gwagwarmaya


 

 

Tags