Iran Ta Bukaci Pakistan Da India Su Kai Zuciya Nesa A Sabaninda Ke Tsakaninsu.
Gwamnatin kasar Iran ta yi kira ga kasashen India da Pakistan su kai zuciya nesa a sabanin da ya shigo tsakaninsu a baya-bayan nan.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasimi ne yayi wannan kira a yau a nan Tehran.
Qasimi ya kara da cewa, kasar Iran a matsayinta na kasa wacce ta fi ko wace kasa a yankin cutuwa da hare-haren ta'addanci ta yi imanin cewa tattaunawa tsakanin kasashen biyu ne kadai hanyar warware matsalar hare-haren ta'addanci wacce ta taso tsakanin kasashen biyu a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Kafafen yada labarai na kasar India dai, sun nakalto labaran da suke nuna cewa jiragen yakin kasar Indina sun kar farmaki kan wasu wurare a cikin kasar Pakistan a safiyar yau talata, inda suka kashe mutane da dama.
A kasar Pakistan kuma, kungiyoyi da jami'an gwamnatin kasar sun yi Allah wadai da hare-haren na kasar India a cikin kasar Pakistan, a yayinda Firai ministan kasar Imran Khan ya kira taron gaggawa na masu fada a ji na kasar don tattauna batun hare-haren na kasar ta India.