Feb 27, 2019 07:53 UTC
  • Rauhani: Al'ummar Iran Za Su Karya Lagon takunkuman Amurka

Shugaba Hassan Rauhani na Iran ya bayyana cewa, da sannu al'ummar kasar Iran za su karya lago dukkanin takunkuman da Amurka ta kakaba wa kasarsu.

A lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yammacin jiya Talata a babban dakin taron babban bankin kasar Iran a birnin Tehran, shugaba Rauhani ya bayyana cewa, duk da irin takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, hakan bai hana Iran tafiyar da harkokinta ba.

Ya ce baya ga ci gaba da sayar da danyen mai da isakar gas da Iran take yi a halin yanzu haka, a cikin watanni 11 da suka gabata ya zuwa yanzu, Iran ta sayar da kayayyakin da take samarwa ga kasashen duniya da ya kai na kimanin dala biliyan 40.

Ya ce babban abin da Iran za ta kara mayar da hankali a kansa shi ne, ci gaba da gudanar da ayyuka na bunkasa harkokin tattalin arziki a bangarori da ba na man fetur ba.

 

Tags