Feb 28, 2019 06:23 UTC
  • Iran Ta Kirayi Kasashen Pakistan Da Indiya Da Su Kai Zukata Nesa

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif ya tattauna da wayar tarho da takwaransa na Pakistan Mahmud Kurashi inda ya bukaci ganin an kai zuciya nesa.

Bugu da kari ministan harkokin wajen na Iran ya kuma bayyana cewa; kasarsa a shirye take ta taimaka wajen ganin an sami zaman lafiya mai dorewa da samo hanyar warware sabanin da yake a tsakanin Islamabad da New Delhi.

Har ila yau ministan harkokin wajen na Iran ya kirayi  kasashen biyu da su  zauna akan teburin tattaunawa.

A gefe daya, ministan harkokin wajen na Iran zai kuma tattauna da takwaransa na kasar Indiya a wani lokaci nan gaba domin karfafa shi akan batun zaman lafiya.

Daga shekaran jiya Talata zuwa jiya Laraba kasashen biyu sun yi musayar kai wa junansu hare-hare da jiragen sama na yaki.

 

Tags