Feb 28, 2019 06:26 UTC
  • Iran : Jagora Ya Yi Fatan Kafa Alaka Mai Karfi Da Armenia

Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Yi Fatan Ganin An Kafa Alaka Mai Karfi Da Kasar Armenia.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gaba da  Pira Ministan  kasar Armenia Nikol Pashinyan a jiya Laraba anan birnin Tehran ya jaddada muhimmancin bunkasa alakar tattalin arziki da ta kasuwanci a tsakanin kasashen Iran da Armenia,tare da yin ishara da kyakkyawar alakar da take a tsakanin Iraniyawa da al’ummar Armeniyawa ‘yan kasar Iran.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma bayyana cewa; Amurkawa ba a bin dogaro da su ba ne, domin ba su da wani aiki da su ka sanya a gaba sai hada fitintinu.

A nashi gefen Pira ministan na kasar Armenia ya yaba da yadda Iran ta ba da dama ga al’ummar Armenia suke gudanar da harkokinsu cikin walwala a Iran, sannan kuma ya bayyana fatansa na ganin alakar kasuwanci a tsakanin kasashen biyu ta bunkasa.

 

Tags