Mar 05, 2019 05:02 UTC
  • Jagora: Kada Ku Bata Lokaci Tare Da Turawa Dangane Da Kyautata Tattalin Arzikin Kasa

Jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khaminae ya bukaci gwamnatin kasar ta rage dogaro da kasashen Turai don kwatata tattalin arzikin kasar

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana  haka ne a lokacinda yake ganawa a kebe da shugaban kasa Dr Hassan Ruhani da kuma majalisar Ministocin sa. 

Jagoran ya kara da cewa a lokacinda gwamnatin Amurka ta janye daga yerjejeniyar Nukliya ta shekara ta 2015, ta kuma maida takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar, su turawa sun yi kokarin kodaitar da kasar Iran don ta ci gaba da mutunta yerjejeniyar, amma ba tare da gabatar da wani abu wanda zai ja hankalin kasar Iran ba. 

Don haka turawa ba abin dogaro bane, dole ne mu nemi wasu hanyoyin da zamu warware matsalolin tattalin arzikin kasar ba tare da dogaro da su ba. 

 

Tags