Mar 09, 2019 10:33 UTC
  • Jagora : Al'ummar Musulmi Na Son Farfado Da Musulinci

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamnei, ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, hankalin duniyar musulmi ya koma kan yadda za'a sake farfado da koyarwar musulinci.

Ayyatollah Sayyid Ali Khameini ya kara da cewa, a'ummar musulmi suna kallon jamhuriyar musulmi ta Iran a matsayin abun koyi.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin da ayke ganawa da da jami'an cibiyarilimi a nan birnin Tehran.

Ayatollah Sayyid Khameini ya kuma kara da cewa, wajibi ne ga malamai da daliban adini su kasance masu riko da tafarkin juyi domin su zama masuamfani ga kasa.

Tags