Mar 11, 2019 04:18 UTC
  • Iran : Ruhani Ya Fara Ziyarar Aiki A Iraki

shugaban kasar Iran, Dakta Hassan Rohani, ya isa birnin Bagadaza na kasar Iraki inda zai fara wata ziyarar aiki ta kwanaki uku.

A yayin ziyarar shugaba Ruhani, zai gana da fira ministan Iraki, Adel Abdel Mahdi, da kuma shugaban kasar ta Iraki Barham Saleh da kuma Ayatollah Ali Sistani.

Wannan dai ita ce ziyara irinta ta farko da shugaba Ruhanin zai kai Irakin, tun bayan hawansa mulki a shekara 2013.

Dama kafin hakan ministan harkokin wajen kasar ta Iran, Mohammad Jawad Zarif, ya isa birnin Bagadaza domin share fagen ziyarar.

Iran ita ce kasa ta biyu wajen huldar kasuwanci da Iraki, bayan Turkiyya, inda kasashen biyu ke son fadada kasuwancinsu zuwa dala Biliyan ashirin a ko wacce shekara.

Tags