Mar 12, 2019 07:46 UTC
  • Karon farko da aka taba baiwa wani jami\\\\\\\'in soji a Iran, irin wannan lambar ta yabo tun bayan juyin juya halin musulinci
    Karon farko da aka taba baiwa wani jami\\\\\\\'in soji a Iran, irin wannan lambar ta yabo tun bayan juyin juya halin musulinci

Jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, ya karrama Janar Ghassem Soleimani, da lambar yabo ta ''Zulfiqar" lambar yabo mafi girma a aikin soji a kasar.

Wannan shi ne karon farko da aka taba baiwa wani jami'in soji a Iran, irin wannan lambar ta yabo tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar a 1979.

Janar Soleimani, shi ne babban kwamandan rundinar kare juyin juya halin musulinci a bangaren yaki na ketare, msuamman a yakin da kasar take da 'yan ta'adda na Da'esh a kasashen Siriya da Iraki, wanda hakan ya sanya yana daga cikin mutanen da ake ganin kimarsu da darajarsu a Iran.

A tarihin musulinci ''Zulfiqar" sunan ne da ma'aikin Allah (SAW), ya sanyawa takoba mai baki biyu ta Imam Ali (AS).

Tags