Mar 14, 2019 04:12 UTC
  • Sharhi : Ziyarar Ruhani A Iraki

Shugaban kasar Iran Dakta Hassan Rohani, ya kammala ziyarar kwanaki uku da ya yi a kasar Iraki.

A ranar Litini data gabata ne shugaba Rohanin, ya isa Bagadaza fadar gwamnatin ta Iraki, inda ya samu kyakyawan tarbe daga mahukunta dama sauren bangarorin al'ummar kasar.

Ana kallon wannan ziyarar ta Ruhani, a wani matsayin babban sako ga Amurka, da 'yan mashin shatanta a yankin, duba da takunkuman data kakabawa Iran, basu hana ta ba karfafa alakatar ta ba da makotanta irinsu da Irakin da kuma sauren kasashen yankin ba.

A yayin ziyarartasa shugaba Ruhanin ya bayyana cewa kasashen biyu zasu ci gaba da karfafa alakar dake tsakaninsu, wacce bata da musali.

Kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama da suka hada da makamashi, sufiri, noma, masana'antu da kiwan lafiya, da dai saurensu.

Shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Rohani ya bayyana cewa alaka tsakanin kasashen Iran da Iraki, alaka ce da dan uwantaka dake da dadadden tarihi.

A yayin da yake amsa tambayar manema labarai a birnin Bagdaza a marecen ranar Litinin, shugaba Rohani na jamhoriyar musulinci ta Iran ya bayyana jin dadinsa kan irin tarben da ya samu daga al'umma da mahukunta kasar Iraki, sannan ya ce alaka tsakanin kasashe biyu nada dadadden tarihi tare da dan uwantaka.

Yayin da yake ishara kan yadda al'ummar kasar Iran ta kasance tare al'ummar Iraki cikin mawuyacin hali da kuma bayar da duk wani taimakon da ya dace, shugaba Rohani ya ce samun tsaro da konciyar hankali na kasar Iraki na a matsayin bunkasar samun zaman lafiya da tsaro ga kasar Iran.

Shugaba Rohani ya tabbatar da cewa babu yadda za a samu tsaro da bunkasar yankin ba tare da taimakon kasashen Iran da Iraki ba, kuma a halin da ake ciki yanzu kasar Amurka ta kakabawa al'ummar Iran takunkumin zalinci da ya sabawa dokokin kwamitin tsaro na MDD domin karin matsin lamba da kuma shiga tsakanin kasashe aminai, domin haka, shugaba Rohani ya bukaci mahukuntan kasashen biyu da su kara karfafa alakar dan uwantakar dake tsakaninsu.

A karshe, Shugaba Rohani ya bayyana amincewarsa da yadda tawagar kasarsa ta samu karbuwa daga mahuntan kasar ta Iraki.

A yayin ziyarar tasa shugaba Ruhani ya gana da dukkan bangarorin jami’an kasar ta Iraki.

Daga cikin manyan jami’an Irakin da shugaban Ruhani ya gana dasu, akwai  fira ministan kasar, Adel Abdel Mahdi, da kuma shugaban kasar Barham Saleh da kuma Ayatollah Ali Sistani, da dai saurensu.

A safiyar jiya Laraba ne Shugaban jamhoriyar musulinci ta Iran Dakta Hassan Rohani ya kai ziyara gidan babban marja'in mabiya mazhabar shi'an na kasar Irakin Ayatollahi sayyid Ali Sistani inda suka tattauna.

Haka zalika kuma Shugaba Ruhanin ya kai ziyara a hubbarin Imam Ali (a.s).

A wani batu kuma mahukuntan Iraki da Iran sun amince da bayar da visa kyauta ga 'yan kasashensu.

Sabanin ziyarar da shugaban kasar Amurka  Donald Trump ya kai a watan Disamba cikin dare a boye ba tare da ma sanin mahukuntan kasar Irakin ba, wanda aka danganta da keta hurumin kasar, shugaba Ruhani na Iran ya samu kyaukyawan tarbe daga bangarori daban daban na Irakin da kuma mahukuntanta.

Iran ita ce kasa ta biyu wajen huldar kasuwanci da Iraki, bayan Turkiyya, inda kasashen biyu ke son fadada kasuwancinsu zuwa dala Biliyan ashirin a ko wacce shekara.

Tags