Mar 15, 2019 16:52 UTC
  • Limamin Juma'ar Birnin Tehran: Amurka Ta Sha Kayi A Kasashen Iraki Da Siriya

Limamin da ya jagoranci sallar juma'ar birnin Tehran ya ce kowa ya yarda cewa jamhoriyar musulinci ta Iran ta karya kudurin Amurka a kasashen Siriya da Iraki

Ayatollahi Muhamad Imami kashani cikin khodubar sallar juma'a ta wannan mako ya bayyana cewa sun yi amfani da dukkanin karfin da suke da shi  wajen karin matsin lamba ga al'ummar kasar Iran, sannan ya kara da cewa domin karya lagon wannan matsin lamba da takunkumin zalincin da aka kakabawa al'ummar Iran, to dole ne gudanar da jagoranci na gari, domin karya dukkanin manufofin Amukra da makiya a kan al'ummar Iran.

Yayin da ya koma kan bikin tsagayowar cikar shekaru 40 da juyin halin musulinci a nan kasar Iran, limamin da ya jagoranci sallar juma'a na birnin Tehran ya ce fitowar da milyoyin al'ummar kasar Iran suka yi a jerin gwano na ranar 22 ga watan Bahram ya karya lagon makircin makiya.

A yayin da yake ishara kan bayyanin jagoran juyin musulinci na Iran Ayattollahi sayyid Aliyu khaminai na cewa lokaci ya yi da juyin musulinci na biyu ya yi, ya ce tushen wadanda ake nufi da wannan khuduba sune al'ummar musulmi da matasan kasar Iran, da ya zama wajibi a kansu su kara zage damtse wajen tabbatar da wannan bayyani na sheraru 40 da suka gabata.

Har ila yau Ayatollahi Imami Kashani ya yi allah wadai da harin ta'addancin da aka kai masallatai biyu a kasar New-Zeland, inda ya ce wannan hari ya nuna makiyan musulinci kaskantu ne.