Mar 17, 2019 09:36 UTC
  • Iran Ta Mika Sakon Ta'aziya Ga Gwamnatin Zimbabwe

Kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran ya mika ta'aziyarsa ga gweamnati da al'ummar kasar Zimbabwe, biyo bayan aukuwar guguwar iska da ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasar

Cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Lahadi, kakakin ma'aikatar harakokin wajen kasar Iran Bahram Qassemi ya mika ta'aziyar hukumomi da al'ummar kasar Iran ga gwamnati da kuma al'ummar kasar Zimbabwe sanadiyar aukuwar guguwar iska mai mai karfi da ta wakana a kasar ta Zimbabwe a jiya assabar.

Sanarwar farko  ta ce an samu gawawwakin mutane 15 , yayin da kuma guguwar ta tafi da mutane akalla 100, wadanda babu duriyarsu.

Ko baya ga hakan guguwar iskar mai lakabin Idai ta yi sanadiyar katsewar wutar lantarki da kuma rusa gidaje masu yawa a kasar.

Tags

Ra'ayi