Mar 02, 2017 19:13 UTC
  • Yemen: Saudiyya Na ci gaba Da Tafka laifukan Yaki A Tare Da Gobon Bayan Amurka.

Yeman ta ce laifukan yakin da Saudiyya ta ke yi a kasar, tare da cikakken goyon bayan Amurka ne.

Shugaban majalisar koli ta siyasa a kasar ta Yemen, Salih Samad,  ya bayana haka ne a yayin ganawa da mataimakin shugaban Majalisar Dinkin Duniya Akan Ayyukan jin Kai Stephen Obrein a birnin Sanaa  a yau alhamis.

Bugu da kari, Salih Samad ya yi ishara da wahalhalun da al'ummar ta Yemen, ta ke sha, saboda hare-haren na Saudiyya, sannan ya yi kira ga duniya da ta goyi bayan kasarsa.

Shugaban majlisar koli ta siyasar kasar Yemen, din ya kuma ce; Hare-haren da Jiragen yakin Saudiyya su ke ci gaba da kai wa yankunan fararen hula da wuraren zaman makoki da wuraren biki, da makarantu da asibitoci, ana yinsu ne da jiragen yakin Fa-16 na Amurka da kuma bama-baman kasar Birtaniya da Amurkan, abinda ya kara jefa al'ummar ta Yemen cikin shan wahala.

Har ila yau, Salih Samad ya yi kira da a kawo karshen  killace kasar Yemen da aka yi da kuma kale jirage suna sauka a filin saukar jirage na Sanaa.

A cikin watan Maris ne na 2015 ne dai Saudiyya ta shelanta yakin akan al'ummar Yemen, da kawo ya zuwa yanzu ya ci rayuka fiye da 10,000 bisa alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

Tags