Sep 25, 2017 19:37 UTC
  • Tsohon Fira Ministan Iraki Ya Ce: Kokarin Ballewar Kurdawar Iraki Shelanta Yaki Ne Kan Kasar

Tsohon fira ministan Iraki kuma mataimakin shugaban kasa a halin yanzu Nuri Al-Maliki ya bayyana cewa: Zaben jin ra'ayin jama'a da al'ummar Kurdawar Iraki suka gudanar kan neman ballewa daga kasar yana matsayin shelanta yaki ne kan hadin kan al'ummar Iraki.

A tsokacinsa dangane da zaben jin ra'ayin jama'a da al'ummar Kurdawar Iraki suka gudanar a yau Litinin kan neman ballewa daga kasar: Tsohon fira ministan Iraki kuma mataimakin shugaban kasar a halin yanzu Nuri Al-Maliki ya jaddada cewa: Zaben jin ra'ayin jama'a da al'ummar yankin Kurdawar Iraki suka gudanar a yau Litinin baya da wani muhimmanci ko kima, kawai dai kokari ne na barazana ga hadin kan al'ummar kasar da ke dauke da sako mai hatsari a nan gaba.

Nuri Al-Maliki ya kara da jaddada bukatar kakaba takunkumi kan shugabannin masu rajin neman ballewa daga kasar Iraki tare da jadada yin kira ga kasashen da suke adawa da ballewar Kurdawan kan su dauki matakin aiwatar da takunkumin siyasa, tattalin arziki da tsaro kan yankin Kurdawan. Kamar yadda Nuri Al-Maliki ya yi gargadin cewa akwai yiyuwar yankin Kurdawan ya zame fagen kulla makirce-makircen kasa da kasa kan kasar Iraki da ma kasashen yankin baki daya.

Har ila yau Nuri Al-Maliki ya yi kira ga al'ummar Larabawa da na Kurdawa da sauran marassa rinjaye a Iraki da su hanzarta daukan matakin rusa makircin kokarin raba kasar ta Iraki saboda makirci ne da ke samun cikakken goyon bayan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila. 

Tags