Nov 20, 2017 10:02 UTC
  • Kotun Kolin Iraki Ta Soke Zaben Yankin Kurdistan

Kotun koli a Iraki ta sanar da soke zaben yankin Kurdistan da aka gudanar a watan Satumba da ya gabata.

A bayyanin data fitar yau Litini, kotun ta ce zaben raba gardama na ballewar yankin Kurdistan da aka gudanar ya sabawa kundin tsarin mulki.

Sannan kotun ta soke duk wasu kudurori da sakamakon zaben na ranar 25 ga watan Satumba da ya gabata.

Soke zaben na Kurdistan na daya daga cikin sharudan da gwamnatin Bagadaza ta gindaya kafin shiga tattaunawa, a yayin da gwamnatin Erbil ta ki amunce sake tattauna batun zaben da ya samu amuncewa da gagarimun rinjaye.

 

Tags

Ra'ayi