Feb 25, 2018 08:10 UTC
  • Sukan Da Jam'iyyun Adawa Na Kasar Jamus Sukewa Gwamnatin Kasar Kan Sayarwa Saudia Da Kawayenta Makamai

Jam'iyyun adawa a kasar Jamus sun yi ta suka kan yadda gwamnatin kasar take sayarwa kasar Sa'udiya da kawayenta a yakin Yemen makamai, duk tare da sanin irin laifuffukan yakin da suke aikatawa a kasar.

Jaridun Kasar Jamus da dama sun nakalto shuwagabannin jam'iyyun adawa na kasar, wadanda suka hada da Sethfan Libish na "Jam'iyya mai matsakaicin ra'ayi ta Jamus" yana cewa, manya-manyan jam'iyyu masu mulki sun yi banza da su a kan wannan matsalar sayarwa kasar Saudia da kawayenta makamai, sun yi gabansu su na sayarwa wadannan kasashe makamai, duk tare da zargin da ake masu na aikata laifuffukan yaki a yakin da suke yi a kasar Yemen. 

Banda haka, akwai wasu jam'iyyun adawa biyu "Libral Demecratic"  da kuma "Alternative to Germany" duk sun yi kakkausar suka kan sayarwa kasashen Saudia da kawayenta makamai, da ma wasu kasashen da suke fama da tashe-tashen hankula a cikin kasashensu a yankin gabas ta tsakiya. 

A rahoton da gwamnatin kasar ta Jamus ta fitar na kasashen da za ta sayarwa makaman, kasar Saudia da wasu kawayenta a yakin da take jagoranta a kasar Yemen suna ciki. rahoton ya kara da cewa Saudia za ta sayi makamai  daga kasar ta Jamus wadanda kimarsu ya kai Euro miliyon 254, sai Masar wacce zata sayi makamai wadanda kimarsu ya kai Euro  miliyon 708 sannan kasar Emmerate ko "Hadaddiyar Daular Larabawa" wacce zata sayi makamai na Euro 214. 

Jurgen Triton, fitaccen dan siyasa, dan jam'iyyar "Green Party" ta kasar Jamus, ya bayyana cewa jam'iyyu masu mulki a kasar sun riga sun gama shirye-shiryen mikawa gwamnatin kasar Saudia kananan jiragen ruwan yaki 33 nan gaba kadan, bayan sun rufe idonsu a kan laifuffukan yaki da taake hakkin bil'adama wadanda kasar ta saudia da kawayenta suke aikatawa a kasar Yemen. Triton ya kara da cewa mafi yawan wadanda suke wahala a yakin da kasar saudia take jagoranta a kasar Yemen yara kanana da kuma farren hula maza da mata. Yakin ne ya jawo yaduwar yunwa a cikin miliyoyin mutanen a kasar saboda kofar ragon da suka yiwa kasar.

Masana dai suna ganin kasar Jamus ta rufe idanunta kan wadanan laifuffukan ne, don ita ma ta sami rabonta a cinikin makamai wanda sauran kawayenta na kasashen turai da Amurka suke yi a kasashen gabas ta tsakiya. Ko ba kome, da wadannan kudade zata kyauta tattalin arzikin kasar ta Jamus. Don haka ne, ita ma kasar Jamus, kamar sauran manyan manyan kasashen duniya, take kokarin ganin ta tallafawa shuwagabannin wadannan kasashe, wajen murkushe abokan gabansu na cikin gida don ganin sun ci gaba da wanzuwa kan kujererun iko da kasashensu.

A wani bangaren masana suna ganin, gasar sayawar kasashen Larabawa makamai wanda kasashen yamma suke yi ya na kara rura wutar fitina da kuma yin kafar angulu ga zaman lafiya a yankin ne. don daga karshe wadannan makamai zasu kare ne kan mutanen wadan nan kasashe ne. Wadanda suke neman hakkokinsu, ko kuma makobtansu. Musamman ganin irin yadda sabani mai tsanani yake kunnu kai a tsakanin kasashen Larabawa, musamman na kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa.  

  

Tags