May 12, 2018 19:29 UTC
  • Iraki:Ana Gudanar Da Zaben 'Yan Majalisa Ba Tare Da Wata Matsala Ba

Ma'aikatar cikin gidan Iraki ta sanar da cewa babu wata matsala ta tsaro da aka samu a yayin da al'ummar kasar ke ci gaba da zaben wakilansu na Majalisar dokoki.

Kafar watsa labaran AlQad ta nakalto kakakin ma'aikatar tsaron kasar Iraki cikin wani bayyani da ya fitar a wannan asabar  ya ce kwamitin tsaro na zaben kasar tare da kwamitin koli na zaben kasar suna gudanar da aiki tare domin sanya ido kan yadda zaben 'yan majalisar ke gudana, kuma ya zuwa lokaci da ya fitar da wannan rahoto babu watsa matsala da ta shafi tsaro da aka gabatar musu.

Sa'o'i kadan bayan fara zaben 'yan majalisar dokoki a kasar, Piraminista Haidar Abadi ya dake doka kai kawo na motoci da kuma rufe filayen sauka da tashi na jirage a jahohin kasar ta Iraki.

Da misalin karfe bakwai na safiyar wannan asabar ne aka fara zaben 'yan majalisar dokokin kasar Iraki a fadin kasar gaba daya. wannan zabe na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a yau asabar  shi ne irinsa  na biyu bayan janyewar Dakarun Amurka daga cikin kasar ta Iraki a shekarar 2011, kuma shi ne na hudu bayan faduwar gwamnatin Saddam Husain a shekarar 2003.

Tags