May 12, 2018 19:29 UTC
  • Harin  Jiragen Kawancen Amurka Ya Hallaka Fararen Hula 17 A Siriya

Tashar talabijin din kasar Siriya ta sanar da mutuwar mutane 17 a wani harin wuce gona da iri da jiragen kawancen kasa da kasa karkashn jagorancin Amurka bisa da'awar yaki da 'yan ta'addar ISIS a kasar

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya nakalto tashar talabijin din kasar Siriya na cewa jiragen yakin kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka bisa da'awar yaki da ta'addanci a kasar sun kai hari kauyen Hamadi dake yankin Haska na arewa maso gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 17.

Hukumomin birin Damuscus sun yi sha yin alawadai da zaman dakarun Amurka a cikin kasar inda suka bayyana hakan da take hurumin kasar.

A bangare guda bayan da sojojin Siriya suka tsarkake kauyukan Baitu-Saham, Yalida, da Bibila a kudancin Damuscus tare kafa tutar kasar a kauyukan, dariruwan iyalai na al'ummar yankin suka fara komawa gidajensu cikin murna tun a wannan safiya ta assabar.

Bisa yarjejjeniyar da dakarun siriya tare da kungiyoyin dake dauke da makamai gami da 'yan ta'adda suka cimma a kudancin birnin Damuscus, a jiya Juma'a 'yan ta'addar sun fice daga wadannan yankuna.

Tags