May 19, 2018 12:09 UTC
  • Ci Gaba Da Murkushe Masu Rajin Kare Hakkin Bil-Adama A Kasar Saudiyya

Mahukuntan Saudiyya suna ci gaba da kokarin murkushe 'yan adawar siyasa, masu rajin kare hakkin bil-Adama da kuma malaman addini da suke bayyana rashin amincewarsu da sabon salon siyasar kasar.

Rahotonni sun bayyana cewa: Jami'an tsaron Saudiyya sun yi awungaba da Sheikh Muhammad Al-Muhsini limamin Masallacin Al-Rajhi da ke birnin Makkah tare da daya daga cikin 'ya'yansa kan zargin sukar sabon salon siyasar mahukuntan kasar.

Tun a cikin watan Satumban shekara ta 2017 ne Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman ya bada umurnin sanya kafar wando daya da duk mai adawa da sabuwar siyasarsa a kasar musamman bude wajajen sharholiya da yin watsi da al'adar wahabiyanci.  

Tags