Jul 18, 2018 18:13 UTC
  • An Gano Tarin  Makaman Isra'ila A Yankunan Da Aka Tsarkake Na Siriya

Dakarun tsaron Siriya sun gano tarin makaman Isra'ila a hanun 'yan ta'adda yayin tsarkake yankin Akrab na gefen kudancin Hamah.

Kamfanin dillancin labaran Sana ya habarta cewa Dakarun tsaron siriya sun sanar a wannan laraba cewa sun gano tarin makamai na haramtacciyar kasar Isra'ila a yankunan da suka tsarkake daga 'yan ta'adda, daga cikin irin wadannan makamai har masu sarrafa kansu da kuma na'urorin sadarwa na aikin soja da 'yan ta'addar ke amfani da su wajen karbar umarni ko wani rahoto  na leken asiri daga Sojojin Isra'ila.

A makuni biyu da suka gabata, tashar talabijin din Al-alam ya nakalto Dakarun siriyan na cewa bayan da suka fatattaki 'yan ta'adda daga yankunan dake gefen Dar'a sun samu tarin makamai kirar kasashen Amurka, Turai da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Wannan lamari dai ya kara tabbatar da cewa kasashen Amurka, Turai da haramtacciyar kasar Isra'ila sune masu taimakawa 'yan ta'addar da makami  a Siriya.

Tags