Jul 21, 2018 19:08 UTC
  • Sojojin Syria Sun Sake  Kwace Kauyuka  Daga Hannun

Tashar talabijin din Syria ta bayar da labarin cewa; A yayin farmakin kwace kauyukan an kashe 'yan ta'adda da dama tare da lalata manyan makamansu

Rahoton ya ci gaba da cewa; Kauyukan da sojojin su ka kwace suna a cikin yankunan Qunaidara da kuma Dar'a.

Tun a ranar 15 ga watan Yuli ne sojojin na Kasar Sriya suka bude kai farmaki akan 'yan ta'adda da suke iko da yankunan kudancin kasar. Kawo ya zuwa yanzu mafi yawancin garuruwa da kauyukan da suke kudancin Syria a kusa da iyakar kasar Jordan sun fice daga karkashin ikon 'yan ta'adda.

Tun a 2011 ne gwamnatin Syria take fada da 'yan ta'adda wadanda kasashen turai bisa jagorancin Amurka da kuma Saudiyya suke goyan baya, wnada kuma ya zuwa yanzu ya ci rayukan dubban mutane.

Tags