Jul 25, 2018 06:29 UTC
  •  Sojojin Masar Sun Kai Sumame A Wata Mabuyar Yan Ta'adda A Yankin Sinaa.

Sojoijin kasar Masar Sun kai sumame a wata mabuyar yan ta'adda na kungiyar Daesh yankin Sina inda suka halaka 13 daga cikinsu suka jakata wasu, sannan suka gano makamai masu yawa a mabuyar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto wasu kafafen yada labarai na kasar masar kan cewa sojojin sun kai sumamen ne a kauyen Al-Yasmin kusa da birnin Arish babban birnin lardin Sanaa ta Arewa. Majiyar ta kara da cewa makaman da sojojin suka gano sun hada da bindigogi, boma bomai da aka danasu don tarayarwa da kuma wasu kayan aikinn soje.

Labarin ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka gabata ma sojojin sun kashe komandan dakarun kungiyar ta Daesh mai suna Abu Jaafar Al-maqdisi. 

Tun ranar 9 ga watan Feberun shekaran da muke ciki ne sojojin kasar Masar suka fara wani shiri na musamman don ganin bayan yan ta'adda a yankin na Sinaa. Rahotanni sun bayyana cewa ya zuwa yanzu sojojin sun halaka yan ta'adda kimani 150. 

Tags