Jul 29, 2018 19:04 UTC
  • Jami'an Tsaron Iraki Sun Kashe Wasu Gungun 'Yan Kunan Bakin Wake A Garin Samarra Na Kasar

Jami'an tsaron Iraki sun yi nasarar halaka wasu gungun 'yan kunan bakin wake kafin su kai ga tarwatsa kansu a tsakanin jama'a a garin Samarra da ke arewa da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar.

Majiyar tsaron Iraki a yau Lahadi ta sanar da cewa: Jami'an tsaron Iraki sun yi nasarar harbe wasu gungun 'yan ta'adda hudu da suka yi jigida da bama-bamai da nufin kai hare-haren kunan bakin wake a garin Samarra da ke arewa da birnin Bagadaza fadar mulkin kasar.

Majiyar tsaron ta bayyana cewa: Bayan samun bayanan sirri kan mutanen hudu, jami'an tsaron Iraki sun bi sawunsu har lokacin da suka yi kokarin dakatar da su a wani waje da babu jama'a amma 'yan ta'addan suka yi yunkurin gudu, don haka aka harbe su, kuma nan take bama-bamai da suke jikinsu suka tarwatse.

Har ila yau jami'an tsaron na Iraki sun yi nasarar kama wani dan ta'adda da ya makare jikinsa da bama-bamai da nufin kai harin kunan bakin wake a garin na Samarra, inda rahotonni suka tabbatar da cewa; Kungiyar ta'addanci ta Da'ish ce ta shirya kai hare-haren a garin na Samarra.    

 

Tags