Aug 05, 2018 12:22 UTC
  • Masar: An Kashe 'Yan Ta'adda 11 A yankin Sinaa

Majiyar tsaron Masar ta sanar da cewa; Sojojin kasar sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a yankin al-arish da ke gundumar Sinaa ta arewa wanda ya kare da kashe mutane 11 daga cikinsu.

Jaridar al-Misri al-Yau ta rubuta a bugunta na yau Lahadi cewa; Kwana daya bayan kisan da 'yan bindiga su ka yi wa Sami al-Kashif, wanda dan majalisa ne mai wakiltar yankin na al-Arish, sojoji sun kashe 'yan ta'adda 11.

Rahoton ya ci gaba da cewa jami'an tsaron sun yi nasarar kame makamai masu yawa da suka hada da bama-bamai da wasu makamai.

Wata majiyar tsaro ta ambato shaidun ganin ido suna fadin cewa; Abu ne mai yiyu wa kungiyar "Wilatul Sinaa' ce ta kai wa dan majalisar harin.

Tags