Aug 14, 2018 19:28 UTC
  • Saudiyyah: Wani Malami Ya Mutu Sakamakon Azabtarwa A Hannun Jami'an Tsaro

Wani malamin Ahlu sunnah dan kasar Saudiyay ya mutu a hannun jami'an tsaron kasar, sakamakon azbatrawar da suka yi masa.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, shafukan masu fafutuka da dama a kasa saudiyya sun nakalto cewa, Sheikh Sulaiman Al-Duwaish wanda tun ranar 22 ga watan Afirilun 2016 jami'an tsaro suka saka shi cikin daurin Talala, ya fuskanci azabtarwa mai tsanani a hannun jami'an tsaro, inda a jiya aka samu labarin mutuwarsa.

Bayan nada Muhammad Bin Salman dan gidan sarkin Saudiyya a matsayin yarima mai jiran gado, ya kame mutane da dama ya wurga su gidan kaso, da suka hada da malamai, da lauyoyi gami da masu fafutukar kare hakkokin bil adama da sauransu, sakamakon sukar salon siyasarsa da suke yi.

 

Tags