Aug 22, 2018 06:26 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Kashe 'Yan Ta'adda Fiye Da 100 A lardin Suwaida Na Kasar

Cibiyar Kare Hakkin Bil-Adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe 'yan ta'addan kungiyar Da'ish 105 a lardin Suwaida na kasar.

Cibiyar Kare Hakkin Bil-Adama ta Syrian human rights Watchdog da ke da matsuguni a birnin London na kasar Birtaniya a jiya Talata ta sanar da cewa: A matakin da sojojin gwamnatin Siriya suka dauka na tsarkake yankin Badiyah da ke shiyar arewa maso gabashin lardin Suwaidah a cikin 'yan kwanakin nan sun kashe mayakan kungiyar ta'addanci ta Da'ish 105.

Lardin Suwaidah dai yana shiyar kudancin kasar Siriya ne kuma kusa da kan iyaka da kasar Jordan da a shekarun baya yankin na Suwaida ya zame cibiyar gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasar ta Siriya. 

Tags