Sep 28, 2018 16:48 UTC
  • Sojojin Mamaya Na Isra'ila Sun Kashe Palasdinawa 6

Hukumomin kiwan lafiya a Palasdinu sun sanar da shahadar Palasdinawa shida (6) ciki har da wani matashi dan shekara 14, sanadin harbin bindiga na sojojin mamaya na Isra'ila a zirin Gaza a yau Juma'a.

Shahiddan wadanda suka hada da Mohammed al-Houm, mai shekara14 da Iyad Al-Shaar, mai shekara18 sun rasa rayyukansu ne a harbin bindiga na sojojin mamaya a wani artabu a tsakiya da kuma arewacin yankin zirin gaza kamar yadda kakakin ma'aikatar lafiya na Palasdinun Achraf al-Qodra, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP.

Ya kuma kara da cewa akwai wasu Palasdiwa biyu da suka mutu sanadin harbin bindiga a kai, saidai ba tare da bayyana sunayensu ba kawo yanzu.

Rahotannin sun nuna cewa kimanin Palasdinawa 10,000 ne suka shiga zanga zangar ta yau Juma'a a zirin Gaza.

 

Tags