Oct 02, 2018 11:22 UTC
  • Dan Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutum 7 A Afganistan

Rahotannin daga Afganistan na cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu a lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani wurin gangamin zabe a gabshin kasar.

Bayanai sun ce dan kunar bakin waken ya tayar da bama baman da ya yi jigida dasu ne a tsakiyar jama'a dake halartar gangamin a lardin Nangarhar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane akalla bakwai da kuma raunana wasu.

Wasu majiyoyi na daban sun ce akwia mutane da dama da suka samu munannen raunuka.

A ranar Juma'a data gabata ce aka fara yankin neman zaben 'yan majalisar dokokin kasar dake fama da matsalar tsaro inda kawo yanzu 'yan takara biyar ne suka mutu a hare haren da ake kaiwa gabanin zaben na ranar 20 ga watan nan na Oktoba, a cewar hukumar zaben kasar.

 

Tags