Oct 02, 2018 18:59 UTC
  • Sojojin Gwamnatin H.K.Isra'ila Sun Jikkata Palasdinawa Masu Yawa A Arewacin Garin Ramallah

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan daliban jami'a a arewacin garin Ramallah, inda suka jikkata Palasdinawa masu yawa.

Kungiyar daliban jami'ar Birzeit da ke garin Ramallah a gabar yammacin Kogin Jordan na Palasdinu a yau Talata ta gudanar da zanga-zangar lumana domin jaddada rashin amincewa da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta kokarin maida haramtacciyar kasar Isra'ila da yankunan Palasdinawa da ta mamaye a matsayar kasar Yahudawa.

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun dauki matakin kaddamar da farmaki kan daliban jami'ar ta Birzeit ta hanyar harbi da bindiga da kuma harba iskar gas mai guba lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatan daliban jami'ar masu yawa kuma da dama an kwantar da su a asibiti saboda matsalar shakewa da suka yi sakamakon rashin shakar iska.

Tun a ranar 19 ga watan Yuli ne Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta kada kuri'ar amincewa da kafa kasar Yahudawa ciki har da yankunan Palasdinawa da aka mamaye, kuma Palasdinawa basu da wani hakki a wannan kasar. 

Tags