Oct 14, 2018 06:39 UTC
  • Shirin Majalisar Dokokin Amurka Na Dorawa Kungiyar Hizbullah Ta kasar Lebanon Takunkuman Tattalin Arziki

A cikin makon da ya gabata ne majalisar dattawan kasar Amurka ta fara wani shiri na dorawa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Takunkumi.

Mike Crapo shugaban kwamitin bankunan Amurka a majalisar dattawan kasar Amurka ya bada sanarwan cewa komitinsa ya fara wani shiri na kakabawa kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon takunkumin tattalin arziki. Ya kuma kara da cewa dukkan sanatoci na jam'iyyun Democrats da Republican sun amince da shirin, sai dai daga karshe takunkumin zai zama doka ne idan shugaban kasa ya sanya masa hannu. Mike Crapo ya ce dokar zata shafi yayan kungiyar da kuma kasashen da suke goyon bayanta a yankin. 

Kungiyar Hizbullah dai ta yaki HKI wacce ta mamaye kasar Lebanon a shekara 1982, kuma ta sami nasarar korarta daga kasar a shekara ta 2000. Banda haka ta sami nasara a kan Haramtacciyar kasar a yakin da ta soma a shekara ta 2006. Har'ila yau kungiyar Hizbullah tana daga cikin kawance masu gwagwarmaya da kungiyoyin yan ta'adda a kasashen Lebanon Siriya da kuma Iraqi.

Banda haka ta taka rawar a zo a gani a cikin nasarorin da aka samu a yaki da yan ta'adda masu samun goyon bayan Amurka da kawayenta na kasashen larabawa a wadannan kasashe.

Tamir Pardo tsohon shugaban hukumar leken asiri ta HKI MOSAD ya bayyana cewa, Isra'ila ba za ta sami nasara a kan kungiyar Hizbullah a duk wani fafatawa da zata shiga da ita ba, don ba wata hanyar da ta rage in banda kakabawa kasar Lebanon Takunkuman tattalin arziki.

Sai dai abinda ya bayyana a fili shi ne gwamnatin kasar Amurka tana kokarin shimfida ikonta a yankin kudancin Asia ne bayan da kawancen masu gwagwarmaya suka kawo karshen kungiyar Daesh a yankin. Kuma kakabawan kungiyar hizbullah da kuma Iran takunkuman tattalin arziki ita ce zabin da ya rage mata. 

A maida martani ga shirin na majalisar dattawan kasar Amuraka, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan nasarallah ya ce, kugiyarsa ba ta ajiye kudadenta a bankuna, don haka wannan takunkumin ba zai yi tasiri a kanta ba. Banda haka ya ce shirin kansa wani nau'i ne na yakin cacan baki  kawai kan mutanen kasar Lebanon, don nisantasu daga kungiyar da kuma tsoratasu. Banda haka wannan shirin wata dubara ce ta bawa Amurka hujjar wanzar da samuwar sojojinta a yankin. 

Tags