Oct 21, 2018 18:54 UTC
  • Tashin Bam Ya Hallaka Mutane Da Dama A Garin Idlib Na Siriya

Wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a tsakiyar garin Idlib na kasar Siriya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane 15.

Cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar kare hakin bil-adama ta kasar Siriya, ta ce a safiyar wannan Lahadi wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse kusa da masallacin Rauda dake anguwar Al-Kusoor na tsakiyar garin Idlib dake a matsayin tungar 'yan ta'adda dake samun Turkawa.

Sanarwar ta ce tarwatsewar Bam din ya yi sanadiyar mutuwar mutum 3 da kuma jikkata wasu 12 na daban.

Kungiyar kare hakin bil-adama ta kasar Siriya ta ce daga ranar 26 ga watan Avrilun da ya gabata zuwa yanzu, an hallaka 'yan ta'adda 360 dake yankunan kewayan gariruwar Idlib, Humat da Halab da irin wannan hari.

Bayan kashin da suka sha shekaru biyu da suka gabata a hanun mayakan kwakwarmayar musulinci da Dakarun kasar Siriya, kungiyoyin 'yan ta'addar na Siriya sun amince da komawa lardin Idlib domin rage zubar da jinin fararen hula a kasar, a halin da ake ciki kuma Sojojin kasar Siriya na kokarin tsarkake lardin gaba dayansa daga 'yan ta'addar.

Tags