Oct 31, 2018 12:04 UTC
  • Afganistan : Hatsarin Jirgin Soji Mai Saukar Ungulu Ya Yi Ajalin Mutum 25

Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane 25 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu na soji a yammacin kasar.

Hukumomin yankin sun danganta hatsarin da rashin kyawon yanayi, a daidai lokacin da kungiyar 'yan ta'adda ta Taliban ke cewa ita ce ta kakkabo jirgin a lardin Anar Dara dake yankin Farah a yammcin kasar.

Jirgin dai na dauke da matukansa biyu da fasinjoji 23 ciki harda shugaban majalisar shawara yankin na Farah a cewar wata sanarwar gwamnatin yankin.

Wani mamba a majalisar yankin ya ce jirgin mai saukar ungulu ya yi karo ne da wani abu a lardin na Herat sakamakon rashin kyawon yanayi.

Tags