Nov 04, 2018 19:19 UTC
  • Al-Ihram:Takunkumin Da Amurka Ta Kakabawa Iran Ya Fuskanci Kalu Bale

Jaridar Al-Ihram ta kasar Masar ta ce sabanin da'awar da magabatan kasar Amurka suka yi, takunkumin da suka kakabawa ya yi gaggauwa rushewa, kuma Kasar Iran da kawayenta sune za su samu nasara a wannan fada.

Jaridar ta ce a baya mahukuntan Amurka sun sanar da cewa kafin ranar 5 ga watan Nuwamba za su hana jamhoriyar musulinci ta Iran sayar da man fetir  koda ganga daya a Duniya, a yau kuma mai bawa shugaban Amurka shawara kan harakokin tsaro John Robert Bolton  ya bayyana cewa kasarsa ba a shirye take ba ta yi abokanin mu'amalarta matsin lamba na hana su sayan Man fetir daga kasar Iran.

John Robert Bolton ya ce babu batun juya baya da kuma adawa ga siyasar Amurkan a kan kasar Iran, saidai kasar ta amincewa wasu kasashe da suke kusa da kasar Iran din damar ci gaba da sayan Man fetir din na Iran.

Al-Ihram ta ce babu irin kokarin da magabatan Amurka ba su yi na ganin sun gamasar da wadannan kasashe na su kasance a tare da ita game da takunkumin da ta kakabawa Iran, amma suka ki, wannan na nuni da cewa kasar Iran din ta samu galaba a kan kasar Amurka.

Kasashe kamar su Indiya, Pakistan, da korea ta kudu sun zabi kasancewa da kungiyar Tarayyar Turai na bijerewa takunkumin zalincin da kasar Amurka ta kakabawa jamhoriyar musulinci ta Iran.

 

Tags