Nov 08, 2018 14:57 UTC
  • Rikici Ya Yi Ajalin Mutum 26 A Wani Gidan Kurkukun Tadjikistan

Majiyoyin tsaro a Tadjikistan, sun ce mutum 26 ne suka rasa rayukansu a wani rikici da ya barke a wani gidan yari dake arewacin kasar.

Mutanen da lamarin ya rusa dasu sun hada da fursuna 24, da mai gadin gidan kaso guda da kuma wani sojin kasar.

Gidan kurkukun mai cikaken tsaro dai na kunshe da fursuna da ake tsare da bisa aikata manyan laifuka ciki har da mambobin kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh kamar yadda majiyoyin tsaron suka shaidawa kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP.

Tuni dai gwamnatin kasar ta aike da sojoji domin taimakawa wajen tabbatar da doka da oda a wannan gidan kurkukun dake birnin Khodjent.

A wani labari kuma hukumomin na Kirghizstan sun ce sun karfafa kwararen matakai na tsaro a iyaka da makobciyar kasar Tadjikistan, bayan da jami'an tsaron iyakoki na kasashen biyu suka tattauna kan lamarin.

Tags