Nov 08, 2018 16:17 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Ceto 'Yan Kabilar Druzes Daga Hannun (IS)

Rundinar sojin kasar Siriya ta sanar da cewa wasu 'yan kabilar druzes da kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta yi garkuwa dasu a yankin Suweida dake kudancin kasar.

Kamfanin dilancin labaren kasar ta Siriya na Sana wanda ya rawaito labarin ya ce sojojin kasar sun fafata da 'yan ta'addan inda sukayi nasara ceto 'yan kabilar ta druzes su 19 da suka hada da mata da yara.

Sojojin sun kuma kashe 'yan ta'addan da sukayi garkuwa da mutanen a cewar labarin.

Gidan talabijin din kasar ya nuna wani hoton bidiyo dake nuna mata da yara gewaye da wasu mazaje sanye da kakin soji a kusa da wata motar pick-up a cikin hamada.

A ranar 25 ga watan Yili da ya gabata ne 'yan ta'addan suka sace mutane kimanin 30 galibi yara da mata bayan wani hari da farmaki da suka kai kan 'yan kabilar ta Druzes a yankin na Suceida.

Tags