Nov 26, 2018 10:03 UTC
  • Taliban Ta Kashe 'Yan Sanda 22 A Afganistan

Hukumomi a yammacin Afganistan sun sanar da mutuwar 'yan sanda 22 a wani farmaki da 'yan ta'adda Taliban suka kai a yankin farah.

A wata sanarwa data fitar ta hanyar manhajar telegram, kungiyar ta Taliban ta dauki alhakin kai harin, wanda ta ce a yayinsa mayakanta sun kuma kwashi ganima ta makaman yaki da dama.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da kungiyar ta Taliban ke kai ire iren wadannan hare hare a wannan yankin na Farah dake yammacin kasar. 

Tags