Dec 03, 2018 10:27 UTC
  • Qatar Zata Fice Daga Cikin Kungiyar OPEC

Kasar Qatar ta sanar da cewa zata ficewa daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur a duniya ta (OPEC), a watan Janairu mai zuwa.

Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a birnin Doha, sabon ministan makamashi na kasar Saad Al-Kaabi, ya ce kasar zata ci gaba da fitar da man fetur, amma zata maida hankali kan samar da iskar gas.

Qatar dai na zaman mamba a kungiyar ta OPEC tun cikin shekara 1961. 

Tags