Dec 03, 2018 16:19 UTC
  • Sojojin Siriya Sun Hallaka Wasu 'Yan Ta'adda 270 A Kudancin Kasar

Kakakin sojin kasar Rasha a Siriya, Oleg Makarevich, ya bayyana cewar sojojin Siriya sun sami nasarar hallaka sama da 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Daesh su 270 a wasu hare-hare da suka kai lardin Suwayda da ke kudancin kasar Siriyan.

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rashan ya jiyo kakakin rundunar kasar Rashan da suke Siriya yana cewa: a yayin wadannan hare-haren, baya ga 'yan ta'addan da aka hallaka, har ila  yau sojojin na Siriya sun kwato wani adadi mai yawan gaske na makamai ciki kuwa har da wasu makamai masu linzami masu tarwatsa tankar yaki kerar Amurka guda 12.

Kakakin sojin Rashan ya kara da cewa mafi yawa daga cikin 'yan ta'addan da aka hallaka din sun iso Suwayda din ne daga yankin Al-Tanf wanda ke karkashin ikon sojojin Amurka.

Kafin hakan ma dai sojojin Siriyan sun sanar da kwace yankin na Al-Suwayda daga hannun 'yan ta'addan suna masu cewa a yayin hare-haren sun sami nasarar hallaka Abu Hajar al-Shishani, shugaban 'yan ta'addan na Daesh a yankin.

 

Tags