Dec 31, 2018 05:27 UTC
  • An Dage Zaben Afganistan Da Watanni Uku

Hukumar zabe a Afganistan, ta sanar da dage zaben shugaban kasar da watanni uku.

Tunda farko dai an shirya za'a gudanar da zaben a ranr 20 ga watan Afrilu na shekara mai shirin kamawa, amma a cewar hukumar zaben kasar saboda dalilai na rashin tsaro an dage zaben har zuwa ranar 20 ga watan Yuli na 2019 mai zuwa.

Hukumar ta ce ta tsawaita zaben ne da watanni uku domin samun damar shirya zaben yadda ya kamata.

Dama dai an shi yayata cewa akwai yiyuwar a dage zaben a daidai lokacin da hukumar ta CEI ke shan suka akan yadda ta gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da ya gudana a watan Oktoba da ya gabata.

Bayanai sun nuna cewa zaben 'yan majalisar dokokin da ya gudana ya fuskanci matsaloli da dama da suka hada dana rashin tsaro da rashin kayan aiki da da rashin kwarewa na jami'an zabe da magudi da bacewar akwatinan zabe da dai saurensu.

Ko baya ga hakan har yanzu akwai yankunan da suka hada da Kabul da ake kan jiran sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin wanda ake wa kallon zakaran gwajin dafi na zaben shugaban kasar.

Kasar Afganistan na fama da matsalar tsaro ne mai nasaba da kungiyar taliban, baya ga wata matsalar mai nasaba da kungiyar IS daya soma a shekara 2014.

 

Tags

Ra'ayi