Jan 15, 2019 17:01 UTC
  • Siriya : Sanyi Ya Kashe Yara 15 A Sansanin 'Yan Gudun Hijira

A Siriya, kimanin yara 15 ne mafi yawansu 'yan kasa da shekara guda, suka rasa rayukansu, sanadin matsanancin sanyi.

A rahoton data fitar majalisar dinkin duniya, ta ce matsanancin sanyi da ake fama dashi da kuma rashin kula ta kiwan lafiya, yara akalla 8 ne suka rasa rayukansu a cikin 'yan makwannin nan da suka gabata, a sansanin 'yan gudun hijira na Rokbane dake kudancin Siriya.

Rahoton ya kuma ce akwai wasu yara bakwai da suka mutu a daidai lokacin da iyallensu ke tserewa wata cibiyar mayakan dake ikirari da sunan jihadi a gabashin kasar.

Asusun kula da yara na MDD, cewa da Unicef ya ce 13 daga cikin yaran 'yan kasa da shekara guda ne, duka kuma a cewarsa sanadin matsaloli na rashin lafiya da ake iya magancewa ko riga kafinsu.

Darektan asusun na Unicef a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afrika, Geert Cappelaere, ya ce wannan ba abunda za'a iya lamunta dashi ba ne ko kadan a wannan karni da muke ciki.

Rikicin da kasar Siriya ke fama dashi tun cikin shekara 2011, ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 360,000 tare da jefa wasu milyoyin 'yan kasar cikin halkin gudun hijira ko dai a cikin kasar ko kuma a ketare.

Tags

Ra'ayi