Jan 19, 2019 06:36 UTC
  • Akalla Falasdinawa 30 Suke Ji Rauni Sanadiyyar Harbin Da Yahudawan Sahyoniya Suka Yi Masu A Gaza

Akalla Paladinawa 30 ne suka ji rauni a lokacinda sojojin HKI suka harbesu da bindiga a jiya jumma'a a yankin Gaza

Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran tan nakalto kakakin ma'aikatar kiwon lafiya na yankin Gaza Ashraf Al-Qidra yana cewa da farko yahudawan sun harbi Palasdinawa 14 da albarusai na gaskiya, a lokacinda suke zanga-zangar neman komawa gida kamar yadda suka saba a ko wace ranar Jumma'a.

Al-Qidra ya kara da cewa sojojin yahudawan har'ila yau sun yi harbu kan motocin daukar marasa lafiya ukku, dauke da Palasdinawan da aka ji rauni. Biyu daga cikinsu mallakin kungiyar Hilal Ahmar ta bada agaji na Palasdinawa  a yankin gaza. 

Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun jiwa wasu ma'aikatan jinya rauni da kuma wasu yan jarida.

Tashar Talabijin ta  Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa an raunta mai aiko mata rahoto a yankin na gaza, Ahmed Ghanem  a kafa.

 

Tags

Ra'ayi