Jan 19, 2019 15:44 UTC
  • Siriya : Kawancen Da Amurka Ke Jagoranta Ya Kashe Fararen Hula 6

Rahotanni daga Siriya na cewa, fararen hula shida ne, da suka hada da yara kanana hudu, suka rasa rayukansu a wani hari da kawacen kasa da kasa da Amurka ke jangoranta ya kai a gabashin Siriya.

Harin wanda aka kai da yammacin jiya Juma'a, a lardin Baghouz, dake yankin Deir Ezzor, a yayinsa an kuma kashe mayakan kungiyar (IS) goma, kamar yadda shugaban kungiyar dake sa ido kan al'amuran kare hakkin bil adama ta Siriya (OSDH), Rami Abdel Rahmane, ya sanar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.

An dai kai harin ne kan wani gida dake lardin na  Baghouz, kuma kokorain jin ta bakin kawancen da Amurka ke jagoranta kan lamarin ya cutura a cewar labarin.

Kawancen da AMurkar ke jagoranta ya jima yana musanta kashe fararen hula a hare haren da yake kaiwa.

Harin dai na zuwa ne kwanaki uku bayan harin da ya yi sanadin mutuwar mutane 19 ciki harda sojojin Amurka hudu a yankin Manbij, wanda kuma kungiyar (IS) ta dauki alhakin kaiwa.

Tags

Ra'ayi