Jan 21, 2019 05:09 UTC
  • Siriya Ta Dakile Wani Harin Sama Na Isra'ila

Rundinar sojin kasar Siriya, ta ce makamman kare sararin samaniyarta, sun dakile wani harin sama dana kasa na Isra'ila kan kasar a cikin daren jiya.

Kamfanin dilanci labaren Siriya na SANA, ya nakalto daga wata majiyar soji cewa, ta ce jiragen makiya na Isra'ila sun kai hare hare ta kasa da sama da dama da makamai masu linzami ciki harda wadanda ake iya sarafawa daga nesa, tare da cewa nakamman garkuwa na harin sama na kasar sun kakkabo dayewa daga cikinsu.

Majiyar ta kara da cewa, Israila ta yi amfani da sararin samaniyar Labanon da kuma na Palasdinu wajen kai hare haren, kuma makaman kare sararin samaniyar na Siriyar sun kakkabo gommai daga cikinsu.

Wasu majiyoyi daga Rasha sun ce jigaren yaki Isra'ila kirar F16, guda hudu sun kai harin makamai masu linzami kan filin jirgin saman  kasa da kasa na Damascos, amma makaman kariya na Siriya su kakkabo dukkan makaman, kuma babu wata hasara ta rayuka ko barna da aka samu a yayin harin.

Wannan dai shi ne aro na biyu a cikin wannan shekara da Isra'ila ke kai hari kan kasar ta Siriya.

Isra'ila wacce bata cika yin bayyani ba kan hare haren da take kaiwa Siriya ba, a wannan karo ta sanar da cewa ta kai hari Siriya kan abunda ta danganta da cibiyoyin Iran a kasar ta Siriya.

Tags