Jan 22, 2019 15:37 UTC
  • Harin Taliban Ya Yi Ajalin Mutum 65 A Afganistan

Kungiyar taliban ta dauki alhakin kai wani hari da yayi sanadin mutuwar mutum 65, a wata cibiyar horon jami'an leken asiri dake lardin Wardak a kudancin kasar ta Afganistan.

Kungiyar ta dauki alhakin kai harin ne ta hanyar manhajarta ta watsapp.

Ana dai samun sabani dangane da alkalumman mutanen da lamarin ya rusa dasu, inda a jiya Litini hukumomin lardin na Wardak, ke cewa mutum 12 ne suka mutu kana wasu 20 suka raunana a harin, amma da yammacin yau Talata, ma'aikatar leken asirin kasar ta ce mutum 36 suka rasu kana wasu 58 suka raunana a harin.

Saidai wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, harin ya yi ajalin mutane a kalla 70 tare da raunata wasu sama da 100.

Harin dai ya kasance wani babban koma baya ga jami'an tsaro kasar ta Afganistan wacce dama ta sha fuskantar hare hare makamantan wannan.

Harin na jiya dai an kai shi da wata mota shake da bama-bamai, kafin daga bisani wasu 'yan bingida uku su fito daga wata motar inda suka kusa kai cikin cibiyar horasda jami'an leken dake Wardak su bude wuta kan mai uwa dawabi.

Tags

Ra'ayi