Jan 31, 2019 12:18 UTC
  • Qatar Ta Haramta Kayan Da Aka Kera A Kasashen Saudiyya, Bahrain, UAE Da Masar

Ministan tattalin arziki na kasar Qatar ne ya sanar da haramta shigar da kayan da aka kera a cikin kasashen hudu da su ka killace kasarsa

Ita ma ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Qatar ta sanar da cewa; Daga yanzu an haramta sayen duk wasu kayayyaki da aka kera a cikin kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da kuma Masar.

Bugu da kari kasar ta Qatar ta fitar da jerin sunayen wasu kamfanoni na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa tare da bayyana su a cikin wadanda aka hana yin mu'amala da su ko  ba su kwangila gudanar da wasu ayyuka a cikin kasar.

A ranar 5 ga watan Yuni ne Kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Bahrain da Masar sun kakaba wa kasar Qatar takunkumi tare da killace ta da hana mu'amala da ita

Tags