Feb 09, 2019 11:56 UTC
  • An Yanke Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Yan Ta'adda 7 A Kasar Tunisia

An yake hukuncin dauri na har mutuwa kan yan ta'adda 7 wadanda suke da hannu a hare-haren ta'addanci na shekara ta 2015 a kasar Tunisia

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto babban mai gabatar da kara na kasar ta Tunisia yana fadar haka a safiyar yau Asabar a wani bayanin da ya watsa. 

Babban mai gabatar da karar ya kara da cewa yan ta'addan guda 7 suna da hannu a hare-haren ta'addanci da aka kai a garuruwan Suse da kuma Bado a shekara ta 2015.

Ya kuma kara da cewa kotun ta yanke hukuncin dauri kama daga watanni 6 zuwa shekaru 16 a kan wasu, a yayinsa ta wanke wasu mutane 27 da ake tuhuma daga laifi. Babu wanda aka yankewa hukuncin kisa inji babban mai gabatar a karar. 

A harin ranar 18 ga watan Maris na shekara ta 2015 a cibiyar nuna kayakin tarihi na Bado a cikin birnin Tunis babban birnin kasar ta Tunisia yan yawan shakatawa 21 ne suka halaka da kuma wani jami'an tsaro guda. Sannan a wani harin da yan ta'addan suka kai kan wani Otel a bakin tekun birnin na Tunis yan kasar Britania 30 ne aka kashe. 

Tags