Feb 19, 2019 12:23 UTC
  • Sojojin Sahayoniya Sun Jikkata Palasdinawa 7

A jiya Litinin ne sojojin na haramtacciyar kasar Isra'ila su ka bude wuta akan Palasdinuwa a kan iyaka da Gaza, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane 7 daga cikinsu

Majiyar tattara bayanai ta Palasdinawa ta ce; A ranar Asabar da dare ma, sojojin na Sayahoniya sun yi harbi akan Palasdinawa akan iyaka da Gaza, wanda ya yi sanadin jikkatar Palasdinawa 9

A yankn al-shuja'iyyah dake gabashin Gaza, Palasdinawa masu yawa sun gudanar da Zanga-zangar yin tur da laifukan da 'yan sahayoniyar suke tafkawa akan al'ummar Palasdinu

A yammacin Kogin Jordan, sojojin Sahayoniya sun kai samame inda su ka yi awon gaba da Palasdinwa 6

Da akwai dubban Palasdinawa da suke a cikin gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra'ila da su ka hada da kananan yara masu yawa.

Tags

Ra'ayi