Mar 02, 2019 09:38 UTC
  • Rikicin Siriya  Ya Hallaka Mutum 246 A Watan Favrayun Da Ya Gabata

Masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Siriya sun fitar da rahoton cewa a watan favrayun da ya gabata, rikici tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 246, daga cikinsu akwai kananen yara 54 da mata 50

Kamfanin dillancin Anatolia ya nakalto masu rajin kare hakin bil-adama na Siriya dake zaune a birnin London na cewa a watan favrayun da ya gabata kawancen kasa da kasa na yaki da kungiyar 'yan ta'addar ISIS bisa jagorancin kasar Amurka sun kashe fararen hula 17 daga cikin akwai kananen yara 4 da mata 4, sannan kungiyar ta'addancin ta ISIS ta kashe fararen hula 21 daga cikin akwai kananen yara 2 da mata 3.

Har wa yau rahoton ya ce a wani hari da wasu kungiyoyin dake adawa da gwamnatin kasar Siriya suka kai a kasar, sun kashe fararen hula 5 daga ciki akwai kananen yara 2, sannan akwai wata kungiyoyi da ba a san manufofinsu ba, sun kashe fararen hula 77, daga ciki, akwai kananen yara 11 da mata 22.

Har ila yau rahoton ya ce kungiyoyin turkawa da suka hada da kungiyar PKK sun kashe fararen hula 18 daga ciki akwai kananen yara 4 da mata 4.

Masu rajin kare hakin bil-adama na kasar Siriya sun ce ko baya ga hakan, an azabtar da mutane 26 a watan favrayun da ya gabata.

 

Tags