Mar 02, 2019 09:38 UTC
  • Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Tashin Boma-Bomai A Kasar Somaliya Ya Karu

Wata majiyar jami'an tsaro a kasar Somaliya ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Magadishu ya karu zuwa 15.

Jaridar "Alqudsul Arabi" ta bayyana cewa majiyar ta shaida mata cewa wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren ta'addanci wanda aka kai kan wani Otel a birnin Magadishu babban birnin kasar ya kai 15.

Majiyar ta kara da cewa an ci gaba da fitar da wadanda suka ji rauni a lokacinda ake cikin barin wuta tsakanin jami'an tsaro da yan ta'adda na kungiyar Al-shabab wadanda suka kai harin. 

Banda hala labarin ya kara da cewa gobarar da ta tashi a bayan hare-haren boma-boman ta watsu har zuwa wasu gine-ginen kasuwanci kusa da otel din. 

Wasu majiyoyin sun bayyana cewa wasu yan ta'adda sun yi yunkurin kashe tsohon babban mai gabatar da kara da kasar a harin na ranar Alhamis amma basu sami nasara ba. 

Kungiyar Alshabab dai ta dauki alhakin kai hare-haren na ranar Alhamis. 

Tags